Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labransa dake tare da tawagar majajjata a Saudiyya cewa; Jaridun kasar saudiyya da dama sun kawo labarai dangane da kisan kiyashin da gwamnatin saudiyya take yi wa mabiya mazhabar shi'a na kasar Yeman da jiragen yaki ba kyakkyaftawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin jaridun na kare manufar wahabiyawa ta kokarin kawo karshen mabiya mazhabar shi'a a cikin kasashen musulmi. 493970