Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro kan hadin kan mazhabobin muslunci a birnin Makka mai alfarma, wanda yake samun halartar manyan malamai daga sassa daban –daban na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Makka cewa; An fara gudanar da wani zaman taro kan hadin kan mazhabobin muslunci a birnin Makka mai alfarma, wanda yake samun halartar manyan malamai daga sassa daban –daban na kasashen musulmi. Taron yana yin dubi kan irin muhimmancin da ke tattare da hadin kai tsakanin musulmi, da kuma yadda ya kamata a manta da batutuwa na banbancin mazhabobin da ke cikin muslunci, tare da hada kai tsakanin dukkanin mabiya mazhabobi mabanbanta domin yi wa Musulunci hidima. 496373