Kamfanin dillancin labarin iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; An gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Kuwait, wadda ta kebanci ma'aikatan banki na daga kasashen musulmi daban-daban. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da irin wannan gasa a kasar Kuwait wanda kuma hakan na daya daga cikin ayyukan da cibiyar kula da ayyukan kur'ani mai tasrki ta kasar kan shirya kuma ta gudanar, tare da taimakon gwamnatin kasar. 496971