IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zaman Taro Kan Abincin Halal A Turkiya

14:53 - December 21, 2009
Lambar Labari: 1864242
Bangaren kasa da kasa; za a gudanar da wani zaman taro kan abincin halal a mahangar addinin muslunci a kasar Turkiya a cikin watan Oktoban shekara ta 2010 miladiyya a birnin Istanbul.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; za a gudanar da wani zaman taro kan abincin halal a mahangar addinin muslunci a kasar Turkiya a cikin watan Oktoban shekara ta 2010 miladiyya a birnin Istanbul. Bayanin ya ci da cewa wannan taro zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da za su bayyana ra'ayoyinsu kan yadda ake tantance abincin da aka halasta a Musulunci da kuma wanda ba a halasta ba. 511903

captcha