Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga kungiyar da ke kula harkokin ilmi da al'adun kasashen musulmi ta ISESCO cewa; babbar manufar gudanar da zaman ita ce yin bahasi kan kasafin kudin shekara na na jami'ar muslunci ta Jamhuriyar Niger. Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar tana bayar da kasafin kudin shekara ga jami'ar domin kyautata harkokin karatu, da kuma aikewa da malaman jami'ar zuwa wasu kasashe domin kara yin kwasa-kwasai. Mustafa Ahmad Ali shugaban hadakar jami'oin musulmi zai samu halartar zaman taron. 534403