Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: an wallafa da watsa wani bincike da ya kumshi shafuffuka saba'in da takwas da kuma ofishin yada al'adun kasar Iran a wannan kasa ta Etiophiya ya dauki dawainiyar da nauyin tabbatar da wannan aiki. Wannan bincike da nazari ya kumshi bangaren tarihi na mazhabobi a wannan kasa ,bayyanar Musulunci da kirsitoci a wannan kasa da kuma dangantakar Musulunci da kiristoci a mahangar Musulunci da kuma gajeran tarihin dangantakar bangarorin biyu a matsayinsu na manyan addinan Allah a wannan kasa. Sai kuma dangantakar musulmi da kiristoci a mahangar dokokin wannan kasa a hukuma mai ci .
539437