Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Masar Alyau Sabi'I ta watsa rahoton cewa: a kasar Masar ce za a gudanar da taron kasa da kasa na komitin koli da ke kula da harkokin Musulunci. A wannan zama na kasa da kasa akwai ministocin harkokin addinin Musulunci,masana da manazarta musulmi da kwararru daga kasashe daban-daban na duniya. A zaman bude taron a yau da safe ahmad Nasif firaministan kasar Masar da Muhammad Said Tantawi Sheikuhl Azzahar da mahmud Hamdi Zakzuk ministan harkokin addini a Masar da kuma Muhammad Shahat Aljindi babban sakataren komitin koli na harkokin addini.
542531