Bayan ta nakalto daga majiyar watsa ta labarai ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke kasar Turkiya ta watsa rahoton cewa; babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na sake gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna. Saktaren Ikmalul Din Ihsan Uglan ya bayyana cewa; sabon matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki ya sake fito da hakikanin mummunar manufar yahudawan sahyoniya a fili karara.
550770