IQNA

Taron Kasa Da Kasa A Madina Kan Bayyana Fuskar Musulunci

15:25 - March 15, 2010
Lambar Labari: 1898547
Bangaren kasa da kasa;a birnin Madina ne za a gudanar da taro kan bayyana hakikanin fuska ta Musulunci da bincike kan rashin dangantakar Musulunci da ta'addanci.
Bayan ta nakalto daga jaridar kasar Saudiya Darul Hayat cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyara Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a birnin Madina ne za a gudanar da taro kan bayyana hakikanin fuska ta Musulunci da bincike kan rashin dangantakar Musulunci da ta'addanci.Kuma wannan taro za a gudanar da shi ne a ranekun takwas zuwa goma ga watan Farvardi na shekara mai kamawa ta hijira shamsiya. Muhammad bin Ali Uklan shugaban jami'ar Musulunci ta Madinatul Munawwara a wata hira kan wannan labari ya bayyana cewa: wannan taro an ba shi taken ta'addanci a tsakanin masu tsautsoran ra'ayi na tunani da nazari .Kuma burin taron shi ne bayyana matsayi na tsakatsakiya.



552627

captcha