Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga kafanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA an habarta cewa; an fara gudanar da zaman taro na fikihun addinin Musulunci a birnin Riyad na kasar saudiyya, wanda ke samun halartar malamai daga kasashen muslmi. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin kasashen da ke halartar zaman taron akwai na yankunan Asia, da kuma Amurka gami da Afirka da kasashen yankin tekun fasha. Inda suke gudanar da bahasi kan wasu mas'aloli na fikihun addinin Musulunci.559864