Bangaren siyasa da zamantakewa: babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da suka da babbar murya kan sabon shiri da tsarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na tilastawa Palasdinawa yin gudun hijira daga yankin yammacin Kogin Jodan a wani sabon shiri na yahudawan sahayoniya.
Daga kasar Turkiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya yi Allah wadai da suka da babbar murya kan sabon shiri da tsarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na tilastawa Palasdinawa yin gudun hijira daga yankin yammacin Kogin Jodan a wani sabon shiri na yahudawan sahayoniya. Ikmalul Din Ihsan Uglu ya jaddada cewa; kungiyar hadin kan kasashen musulmi na daukan wannan sabon shiri na sahayoniya a na tilastawa mazauna yankin Palasdinu a yammacin kogin Jodan shiri ne da ked a burin nuna wariya da kawar da wata al'umma daga yanki kuma abin yin Allah wadai ne a fili.
562337