Kamafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na IIDR an habarta cewa, Za a gudanar da wani zaman taro domin yin bahasi kan ayoyin da ke cikin suratul fatiha da sirrin da ke tattare da su, wanda za a gudanar a birnin Manchester na kasar Birtaniya. Ya ci gab ada cewa, taron yana da matukar muhimmanci musamman ma ga musulmi masu nazari kan alkur'ani mai tsarki a kasar ta Birtaniya. Wannan taro dai cibiyar kula da harkokin nazari kan ilmomin kur'ani ta kasar Birtaniya ce ta shirya gudanar da shi a cikin mako mai zuwa. 565083