Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da jaridar kasar Qatar da al-shrq ta buga ta habarta cewa, Ana shirin bude wani bankin musulunci na farko a kasar Faransa daka baiwa suna bankin taisir, wandsa zai rika gudanar da ayyukansa daidai koyarwar musulunci. Bayanin ya kara da cewa wasu daga cikin masu saka hannayen jari daga kasashen musulmi sun nuna matukar yabawarsu da aiwatar da shirin bude wannan banki, wanda zai taimaka musu harkokinsu na kudi a nahiyar turai. 565674