IQNA

Taron Kungiyoyin Musulmi Na Duniya A Istambul Na Turkiya

15:08 - April 27, 2010
Lambar Labari: 1913754
Bangaren kasa da kasa:A birnin Istambul na kasar Turkiya daga jiya biyar ga watan Ordebehesh an fara taron kungiyoyin musulmi na duniya .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga habervakti ta watsa rahoton cewa; A birnin Istambul na kasar Turkiya daga jiya biyar ga watan Ordebehesh an fara taron kungiyoyin musulmi na duniya . a wajen wannan taro an samu halartar jami'an gwamnatin Turkiya day an siyasa da wakilan majalisar dokoki a wannan kasa .Abdul Aziz Usman babban sakataren hukumar kula da ilimi da al'adu na Asesko ya jaddada muhimmancin malamai ,masana da wakilai na kungiyoyi daban daban na gwamnati dab a na gwamnati ba musulmi da malaman jami'a a duniyar musulmi da su yada addinin Musulunci ga duniya baki daya.


568680

captcha