IQNA

An Fitar Da Wani Littafin Wakokin Yabon Manzo (SAW) Da Turkanci

15:55 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940417
Bangaren kasa da kasa; An fitar da wani littafi na wakokin yabon manzon Allah (SAW) a cikin harshen turkanci, wanda wani mawakin classic na kasar Mahmud Kapalan ya rubuta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na ilknokt ya habarta cewa, an fitar da wani littafi na wakokin yabon manzon Allah (SAW) a cikin harshen turkanci, wanda wani mawakin classic na kasar Mahmud Kapalan ya rubuta. Rahoton ya ce tun bayan da addinin muslunci ya yadu a dukkanin sassan da daular Usmaniyya ta shimfida karfin ikonta, 'yan kabilar turk sun yi ta kokari a bangarori daban-daban domin yada addinin muslunci,daga cikin kuwa hard a rubuta littafai da kuma rubuta wakoki daban-daban da ma wadanda ake rerawa, da suka hada da na wayar da kai da kuma na yabon manzon Allah (SAW) a cikin harshen turkanci. 597219
captcha