IQNA

An Kawo Karshen Taron Kasa Da Kasa Na Fasahar Musulunci A Yeman

15:54 - June 15, 2010
Lambar Labari: 1940424
Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin San'a na kasar Yeman kan tarihi da kuma fasar musulunci wanda ya samu halartar masana daga kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Yeman SABA ya habarta cewa, a jiya ne aka kawo karshen taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin San'a na kasar Yeman kan tarihi da kuma fasar musulunci wanda ya samu halartar masana daga kasashen duniya. Rahoton ya ce wadanda suka halarci taron akasarinsu malaman jami'a ne da kuma masu nazari kan tarihin muslunci, inda aka gabatar da laccoci masu bayyana ci gaban da musulunci ya zo wa zamani da shi a cikin tarihi. 596884


captcha