IQNA

Isra'ila Ta Hanyar Zaluntar Palasdinu Ta Fitar Da Fuskar Shadancinta A Fili

11:44 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941446
Bangaren siyasa da zamantakewa; Ayatullahi Kablan na'ibin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi'a a Labanon ya jaddada cewa; Isra'ila ta hanyar aikata zalunci kan al'ummar Palsdinu da killace al'ummar yankin Zirin Gaza ta fito da fuskarta ta zalunci a fili karara kowa na gani tamkar wani butunbutumi a gabansa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga kasar Labanon bayan ta nakalto daga jaridar Al'intigad ta wannan kasa ta labanon ta watsa rahoton cewa; Ayatullahi Kablan na'ibin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi'a a Labanon ya jaddada cewa; Isra'ila ta hanyar aikata zalunci kan al'ummar Palsdinu da killace al'ummar yankin Zirin Gaza ta fito da fuskarta ta zalunci a fili karara kowa na gani tamkar wani butunbutumi a gabansa. Ayatullahi Abdul Amir Kablan ya bayyana haka ne alokacin wani zama day a shafi darussa kan Akhalaki a birnin Beiruti inda y ace yana bukatar musulmi da su taimakawa wadanda ake zalunta da kawo karshen wannan zalunci da tsama tuta daya wajen intar da Kudus.


598269

captcha