IQNA

Batun Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza Ya Zama Batu Na Duniya Baki Daya

16:52 - June 19, 2010
Lambar Labari: 1942488
Bangaren siyasa; Ayatollah Ahmad Jannati day a jagoranci sallajuma a a jiya abirnin Tehran ya bayyana cewa, batun wajabcin kawo karshen killace Gaza Kira na duniya baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatollah Ahmad Jannati da ya jagoranci sallajuma a a jiya abirnin Tehran ya bayyana a gaban dubban daruruwan masallata a masallacin juma'ar birnin Tehran cewa, batun wajabcin kawo karshen killace Gaza Kira na duniya baki daya. Ya ci gaba da cewa yahudawan sahyuniya sun yi zaton cewa za su iya yin yawo da hankulan al'ummomin duniya da batun sassauta killacewar da suke yi al'ummar Gaza. Haka nan kuma ya tabo batun takunkumin da Amurka da 'yan korenta suka kakaba wa Iran ta hanyar yin amfani da kwamitin tsaron majalisar diniin duniya, ya ce wannan bay a da wani tasiri wajen dakatar da Iran daga shirin na makamashin nukiliya na zaman lafiya. 599581



captcha