Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da zaman taron harkokin banki da harkokin kudi na kasashen musulmi, wanda za a gudanar a tsibirin Moris, wanda zai samu halartar masana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, za a fara gudanar da zaman taron harkokin banki da harkokin kudi na kasashen musulmi, wanda za a gudanar a tsibirin Moris, wanda zai samu halartar masana. Bayanin ya ci gaba da cewa mahalarta taron za su mayar da hankali ne kan yadda za a bunkasa harkar kudi da saka hananyen jari na kasashen musulmi. 600231