Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na icied2010 cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a kasar Malazia da zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka shafi koyarwar addinin muslunci. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman abubuwan da taron zai yi dubi a kansu hard a samar da sabbin hanyoyi na zamani, da za a iya yin amfani da su wajen koyar da ilmomin addinin Musulunci a kasashen musulmi. 600882