Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na da hulda da jama'a na ma'aikatar bunkasa harkokin tattalin arziki ta kasar Azarbaijan cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Baku fadar mulkin kasar Azarbaijan kan harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi, wanda ya samu halartar masana daga kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya yi armashi matuka, domin kuwa bangarorin da suka halarci taron sun cimma matsaya kan hanyoyi da dama da za a bi wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi. 602427