IQNA

Shugabannin Majalisun Dokokin Kasashen Musulmi Za Su Yi Zama

19:32 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946901
Bangaren kasa da kasa; Shugabannin majalisun dokokin kasashen musulmi mambobin OIC za su gudanar da zamansu a mako mai zuwa a birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran resalaehhaber an bayyana cewa, Shugabannin majalisun dokokin kasashen musulmi mambobin OIC za su gudanar da zamansu a mako mai zuwa a birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria. Bayanin ya ci gaba da cewa, taron zai mayar da hanakali kan muhimman batutuwa da suka danganci kasashen musulmi musamman ma halin da palastinawa suke ciki a yankin Gaza, da hanyoyin da za a bi wajen tilasta haramtacciyar kasar Isra'ila ta janye killacewar da take yi wa yankin. 604154



captcha