Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga reshen yada labaransa na yankin asia ta tsaka an habarta cewa, shugaban kwamitin kungiyoyin kasashen musulmi na duniya ya yi kira da a kawo karshen rikicin da yake faruwa a kasar Kyrgystan. Bayanin ya ci gaba da cewa kiran ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin sake barkewar wani sabon rikicin a kasar ta Kyrgystan. 604913