Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wani bayani da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ofishin Ayatollah Safi golpaygani an bayyana cewa, daga cikin bayanan da shehin malamin ya gabatar kan zagayowar ranar wafatin Sayyida Zainab (AS) ya fadi cewa, ta yi gagarumar hidima wajen fitar da waki'ar Ashura tare da tabbatar da ita a cikin ramzozi na tarihin Musulunci da ba za a taba manta da su ba. Bayanin ya ci gaba da cewa Sayyida Zainab ba za ta gushe tana misilta ramzi na hakikanin Musulunci ba har kasa ta nade. 605657