Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na sapphire news an bayyana cewa, jagoran kiristocin birnin Strasburg na kasar Faransa ya yi Allawadai da wulakanta kabuburan musulmi da wasu kirista ke yi masu tsattsauran ra'ayi a jahar Alens.
A cikin bayanin da ya fitar ya bayyana cewa gudanar da aiki irin wannan na tsokanar musulmi aiki ne maras kyau, wanda zai iya kawo tashe-tashen hankula, kuma ya saba wa dabi'a da akida ta addinin kirista.
608200