IQNA

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Wani Sabon Musulunta A Tanzania

20:20 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953228
Bangaren kur'ani; Wani mutum dan asalin kasar Tanzaniya da ke zaune a kasar Yeman ya musulunta a garin Adn, bayan ya ambaci kalmomin shahada an ba shi kyautar kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarai da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kasar Tanzania an habarta cewa, wani mutum dan asalin kasar Tanzaniya da ke zaune a kasar Yeman ya musulunta a garin Adn, bayan ya ambaci kalmomin shahada an ba shi kyautar kur'ani mai tsarki tare da wasu abubuwa masu amfani gare shi.

Ma'ikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ce ta dauki nauyin kula da karbar masu karbar Musulunci a kasar, wadanda akasarinsu 'yan kasashen waje ne da suke zaune a kasar.

A cikin yan lokutannan bisa bayanan da ma'aikatar ta bayar, kimanin mutane 3o ne suka karbi addinin Musulunci a garin And na kasar Yeman.

607349



captcha