IQNA

Malazia Za Ta Tura Wata Tawaga Zuwa Yankin Zirin Gaza

20:19 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953231
Bangaren siyasa da zamantakewa; Majalisar malaman addinin Musulunci ta kasar Malazia za ta tura wata tawaga zuwa yankin zirin Gaza ta hanayar ruwa dauke da kayayyakin taimako ga al'ummar yankin da ake killacewa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da kamfanin dillancin labaran ma'a ya bayar ya habarta cewa, majalisar malaman addinin Musulunci ta kasar Malazia za ta tura wata tawaga zuwa yankin zirin Gaza ta hanayar ruwa dauke da kayayyakin taimako ga al'ummar yankin da ake killacewa tun tsawon shekaru uku da suka gabata. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tawaga da ta hada da wakilan kungiyoyin Musulunci da na kare hakkin bil adama na kasar Malazia, za ta kai kayyakin taimako da suka hada da kayan abinci, gini da dai sauran ga al'ummar yankin.

610599





captcha