Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na arabonline an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta mata a birnin Tripoli na kasar Libya a babban dakin taron Fursan da ke babban otel din birnin. Bayanin ya ci gaba da cewa ana gudanar da taron gasar ne bisa taken ayar nan da take kiran musulmi da su yi riko da iggiyar Allah guda daya ka da surarraba.
Yanzu haka dai masu karawa da juna da yawansu mutane 90, kuma na kasa yanayin yadda ake gudanar da gasar zuwa kashi hudu, ta yadda daga karshe za a fitar da wadanda za su kara da juna domin fitar da na daya da kuma nabiyu zuwa na uku da na hudu tsakanin dukknin rukunonin gasar.
612443