Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na hukumar bunkasa al'adu da ilmin musulunci ta Iran cewa, za a gudanar da wata babbar gasa a matsayi kasa da kasa wajen fitar da ababe na fasaha da ke nuni da halin da al'ummar Gaza suke ciki, wadda za a gudanar lardin Golestan da ke cikin kasar.
Ya ci gaba da cewa wannan gasar za ta mayar da hanakali ne wajen bayyana muhimman ababe na fasaha da za su iya yin gagarumin tasiri wajenbayyana wa al'ummar duniya halin da mutanen Gaza ke ciki.
613804