Bangaren kas ada kasa; Za a kafa wani bankin Musulunci na biyu a kasar Kyrgystan, wanda cibiyar harkokin tattalin arziki ta Armana Raya za ta dauki nauyin kafawa tare da kula da shi gami da babban bankin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na inform an bayyana cewa, mataimakin ministan harkokin tattalin arziki da bunkasa masana'antu na kasar Kyrgystan ya bayyana cewa, za a kafa wani bankin Musulunci na biyu a kasar Kyrgystan, wanda cibiyar harkokin tattalin arziki ta Armana Raya za ta dauki nauyin kafawa tare da kula da shi gami da babban bankin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar baki daya.
Ya kara da cewa yanzu haka an kammala da dama daga cikin shirye-shiryen kafa wannan babban banki na Musulunci, wanda zai zama shi ne irinsa na biyu a kasar.
Wannan bankin za a saka masa suna ne Fattah Finance, kamar yadda aka sama na gabaninsa suna Alhilal, wanda kasar hadaddiyar daular larabawa ta jagoranci budewa.
619143