IQNA

Rashin Amincewa Da Gayyatar Geert Wilders Zuwa Jamus

19:42 - July 25, 2010
Lambar Labari: 1962098
Bangaren kasa da kasa; Jam'iyar CDU ta mabiya addinin kirista a kasar Jamus ta nuna rashin amincewarta da gayyatar dan majalisar kasar Holland mai tsananin gaba da addinin musulunci Geert Wilders zuwa kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na harriyet a yanar gizo an bayyana cewa, jam'iyar CDU ta mabiya addinin kirista a kasar Jamus ta nuna rashin amincewarta da gayyatar dan majalisar kasar Holland mai tsananin gaba da addinin musulunci Geert Wilders zuwa kasar ta Jamus.

Bayanin ya ci gaba da cewa jam'iyar ta sanar da hakan ne bayan da wasu daga cikin 'yan jam'iyar suka aike da goron gayyata ga mutumin wanda ya shahara da kiyayya da addinin musulunci, inda jam'iyar ta fitar da bayani da ke nuna cewa ba ta da wata dangantaka da gayyatar, kuma ba ta amince da ita ba.

620293
captcha