IQNA

An Tattara Kur'anai Masu Kuskure A Yankin Kurdistan Na Iraki

19:54 - August 05, 2010
Lambar Labari: 1967449
Bangaren kasa da kasa; An tattara dubban kwafi-kwafi na kur'anai a yankin Kurdistan mai cin gishin kansa a kasar Irakiwadanda aka buga su da kusakurai a cikinsu, wadanda aka buga su a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na kasar Iraki an bayyana cewa, babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar ya bayyana cewa, an tattara dubban kwafi-kwafi na kur'anai a yankin Kurdistan mai cin gishin kansa a kasar Irakiwadanda aka buga su da kusakurai a cikinsu, wadanda aka buga su a kasar Syria a lokutan baya.

Ya kara da cewa akasarin kur'anan da aka tatatra ya zuwa yanzu ahka yankin an Kurdistan an buga su ne a babbar cibiyar buga littafai ta darul mahabba da ke birnin Damascus.

Daga cikin surorin da aka yi kurakuran a cikinsu akwai surat Yusuf, da surat Ibrahim, da kuma surat ra'ad, inda kimanin ayoyi dari Dari daya daga cikin wadan nan surori aka canja musu wurare.

626876



captcha