Bangaren kasa da kasa; Dakarun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun rusa wata makabartar musulmi da ke birnin Qods da ke dambare da masallacin mai alfarma, lamarin da ya jawo fushin al'ummar musulmi daga ko'ina cikin fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da jaridar Kuwait Times da buga an bayyana cewa, dakarun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun rusa wata makabartar musulmi da ke birnin Qods da ke dambare da masallacin mai alfarma, lamarin da ya jawo fushin al'ummar musulmi daga ko'ina cikin fadin duniya baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin lokacin yahudawan sahyuniya sun sha alwashin rushe duk wasu muhimman wurare da ska da dangantaka da al'ummar musulmi ko tarihinsu.
Mohammad Abu Ata daya daga cikin mambobin kwamitin kare masallacin Qods ya bayyana cewa, wannan makabarta tana da kabrukan daruruwan sahabbai da bayin Allah na gari.
631231