Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Kuwait Times an habarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Kuwait ta gina wasu masallatai sabbi guda 25 da nufin dudanar da tarukan addini a cikin watan Ramadan mai alfarma da muke ciki.
Jami'I mai kula da harkokin masallatai a ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait Walid shu'aib ya bayyana cewa, daga cikin ayyukan da za a rika gudanarwa a wadannan masalatai har da ayyukan bayar da taimako ga mabukata.
Ya kara da cewa yanzu haka dai akwai masallatai sama da 1300 a sassa daban-daban na kasar Kuwait, wadanda ake gudanar da tarukan addini a cikinsu.
631126