Kamfanin dillancin watsa labarai da suka shafi Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ya nakalto daga majiyar watsa labarai ta calqubanchi.com ya watsa rahoton cewa; Said Sadrul Din Kabachi limamin juma'ar birnin Najaf Ashraf ya bayyana cewa marigayi Said Abdul Aziz Hakim jagoran majalisar koli ta yan shi'ar Iraki yada daga cikin masu kokari wajen bunkasa hadin kai a tsakanin yan shi'a da sunna a Iraki. Said sadrul Din Kafachi a lokacin hudubar sallar juma'ar day a gabatar a ranar ashirin da biyu ga watan Murdad ne a huseiniyar Fatimiya a birnin Najaf Ashraf ya bayyana hakan.
632705