Bangaren kasa da kasa; An fitar da mujalladi na gima sha daya na tarjamar tafsiril kur'ani mai tsarki na almizan a cikin harshen Turkanci, wanda babban malamin addinin muslunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Muhhammad Tabatabai ya rubuta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Musa Gunes an habarta cewa, an fitar da mujalladi na gima sha daya na tarjamar tafsiril kur'ani mai tsarki na almizan a cikin harshen Turkanci, wanda babban malamin addinin muslunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Muhhammad Tabatabai ya rubuta a lokacin rayuwarsa.
Bangaren da jami'ar Almostafa ta bude dakin ajeye kayyakin tad a bijiro da su a baje kolin kur'ani na duniya a birnin Tehran ne ya kawo littafin wanda aka buga a ciki gaba da tarjama tafsirin na almizan da ake yi a cikin harshen turkanci.
Yanzu haka dai babbar cibiyar da ek kula da harkokin tarajamar littafan addiinin muslunci ta birnin Istanbul ta mayar da hanakali wajen ganin an kammala buga sauran mujalladan littafin tafsin.
634386