IQNA

Zama Akai Akai Kan Kur'ani A Watan Azumi Ramadana A Bahrain

14:00 - August 18, 2010
Lambar Labari: 1976395
Bangaren kasa da kasa;cibiyar addini da al'adu ta Said Amin Bahrain a dalilin fara watan azumin Ramadana tana kaddamar da zama a kai akai kan Kur'ani.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Muzin ta watsa rahoton cewa; cibiyar addini da al'adu ta Said Amin Bahrain a dalilin fara watan azumin Ramadana tana kaddamar da zama a kai akai kan Kur'ani. Said Mahmud almusawi daya daga cikin malamai na kur'ani da masana ya gabatar da jawabi kan bahasin da ya shafi dangantakar dan adam da matakan rayuwarsa.



635271
captcha