Bangaren kasa da kasa; Mukaddashin firaministan britaniya a wani mataki na ganin ya dadawa musulmi da kyautata dangantaka da su a cikin wannan wata na azumin ramadana da kuma samun martani mai dadi a duniyar musulmi a lamarin ambaliyar ruwa a Pakistan ya bayyana cewa; musulmi wajen taimakawa juna abin koyi ne a fadin duniya.
Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta KUNA ya watsa labarin cewa; Mukaddashin firaministan britaniya a wani mataki na ganin ya dadawa musulmi da kyautata dangantaka da su a cikin wannan wata na azumin ramadana da kuma samun martani mai dadi a duniyar musulmi a lamarin ambaliyar ruwa a Pakistan ya bayyana cewa; musulmi wajen taimakawa juna abin koyi ne a fadin duniya. Nek Kalg mukaddashin firaministan kasar Britaniya a ranar talata ce ashirin da shidda ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ya bayyana cewa; ina jinjinawa matakin da hukumar agaji ta kasa da kasa ta musulmi da sanarwar da ta fitar na neman taimako da illahirin musulmi a fadin kasashen duniya da su kawo way an uwansu musulmi a Pakistan dauki bayan da bala'in ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
636460