Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da ake yi wa take da sa'adul fars da ta kebanci mata a kasar Yeman, wadda cibiyar kwamitocin ayyukan kur'ani na kasar kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na Ma'arib press an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da ake yi wa take da sa'adul fars da ta kebanci mata a kasar Yeman, wadda cibiyar kwamitocin ayyukan kur'ani na kasar kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kowace shekara.
Abdullah Abdulilah Salam shugaban cibiyar raya aladu ta kasa, da kan dauki nauyin shirya aikace-aikace na matasa tare da wayar musu da kai harkokin addinin Musulunci ya bayyana cewa, gasar za ta gudana ne kamar yadda aka saba gudanar da ita.
Ya kara da cewa a wannan karon mai yiwuwa gasar ta fi lokutan baya armashi, bisa la'akari da karbuwar da ta samu daga sassa daban-daban nakasar tsakanin mata masu sha'awar karatu da hardar kur'ani mai tsarki.
640400