Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu mutane hudu ne daga cikin wakilan cibiyar addinai ta kasar Turkiya suka halarci baje kolin kayayyakin kur'ani mai tsarki da ke gudana a birnin birnin Tehran, wanda kuma shi ne karo na goma sha bakawai da ake gudanar da irin wannan baje kolin kur'ani na kasa da kasa a birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wakilan cibiyar addinai ta kasar Turkiya ta bude wani daki a wurin baje kolin, inda kawo wasu daga cikin ayyukan fasaha da musulmin kasar Turkiya suka yi na ado da rubutun kur'ani mai tsarki.
640418