IQNA

Tsowon Firaministan Holand Ya Yi Watsi Da Hadin Guiwa Da Jam'iya Mai Adawa Da Musulunci

13:19 - August 28, 2010
Lambar Labari: 1982648
Bangaren kasa da kasa; Daris Wan Agat tsowon firaministan kasar Holand ya yi watsi da duk wani hadin guiwa da Girat Waldarz shugaban jam'iyar yanci mai adawa da Musulunci da musulmi a kasar domin kafa sabuwar gwamnati.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar Zaman ta kasar Turkiya ya watsa rahoton cewa; Daris Wan Agat tsowon firaministan kasar Holand ya yi watsi da duk wani hadin guiwa da Girat Waldarz shugaban jam'iyar yanci mai adawa da Musulunci da musulmi a kasar domin kafa sabuwar gwamnati. Shi dai tsohon firaministan ya yi barazanar cewa matukar aka hada guiwa da wannan jam'iya ta yanci mai nuna tsananin adawa da Musulunci da musulmi a kasar to ko shakka babu zai marabus daga mukaminsa .Har ila yau ya ci gaba da yin barazanar cewa a taron da mambobin kungiyarsa za su yi zaman matukar bas u bada tabbaci na karshen na kin hadin guiwa da wannan iya ba to zai yi marabus daga zama mamba a jam'iyarsa.

642435


captcha