Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na ic-el cewa, Za a gudanar da tarukan dararen lailatul qadr a cibiyoyin Musulunci na kasar Birtaniya, musamamn ma a birnin London fadar mulkin kasar ta Birtaniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin kasar Birtaniya suna gudanar da taruka daban-daban a lokutan azumin watan Ramadan, amma sun fi mayar da hanakali ga ayyukan ibada a lokutan dararen lailatul qadr.
Yanzu haka dai dukkanin cibiyoyin da suke daukar nauyin gudanar da tarukan ibada a dareren lailatul qadr da ke cikin birnin London sun kammala dukkanin shirye-shiryensu kan hakan.
642865