Bangaren kasa da kasa; A ci gaba da daukar daliban addini da jami'ar Al-mostafa (SAW) ta duniya take a kasashen latin Amurka, ya zuwa yanzu ta sheda karbar Musulunci daga al'ummomin kasashe da dama da ke yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantaw ada ta hada shi da tsohon jakadan kasar Iran a kasar Colombia ya bayyana cewa, a ci gaba da daukar daliban addini da jami'ar Al-mostafa (SAW) ta duniya take a kasashen latin Amurka, ya zuwa yanzu ta sheda karbar Musulunci daga al'ummomin kasashe da dama da ke yankin na Latin.
Ya ce ko shakka babu jamia'r Mostafa ta duniya tana taka gagarumar rawa wajen wayar da al'ummomin duniya ta hanyar daukar dalibai daga kasashen duniya daban-daban, wanda hakan ne ya bata damar bayyana hakinanin koyarwar addini a kasashen.
A bayanin nasa sakamakon kokarin da jami'ar take yi an samu karuwar fahimtar addinin Musulunci a kasashen latin Amurka da dama.
644552