Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na Bernama cewa, pira ministan kasar malazia ya kira da a dauki kwararn matakai wajen shiga kafar wando daya da masu cin zarafin addinin Musulunci ta hanyoyin sadarwa na internet.
Wannan bayani ya tabbatar da cewa pira ministan kasar ta Malazia ya nuna matukar fusata kan yadda wasu daga cikin masu kiyayya da Musulunci a cikin kasashen nahiyar turai suke yin amfani da hanyar yanar gizo wajen cin zarafin addin Musulunci.
Ya bukaci bangarorin da ke kula da harkokin sadarwa na yanar gizo a kasar malazia da su su fara gudanar da dukkanin ayyukan da suka dace domin kalubalantar masu aikata wannan aiki.
648598