IQNA

Matasa Sun Nuna Rashin Amincewa Kan Karancin Masallatai A Kosovo

15:00 - September 12, 2010
Lambar Labari: 1991955
Bangaren kasa da kasa; Wasu matasa musulmi da suka gudanar da wani gangami a fadar mulkin kasar Kosovo sun nuna rashin amincewarsu da karancin masallatai da musulmin kasar ke fama da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na yankin Balkan an bayyana cewa, Wasu matasa musulmi da suka gudanar da wani gangami a fadar mulkin kasar Kosovo sun nuna rashin amincewarsu da karancin masallatai da musulmin kasar ke fama da shi a kasar.

Kwamitin matasa musulmi na kasar Kosovo ne ya shirya gudanar da wannan gangani da ya samu halartar matasa musulmi da dama, wadanda suke nuna takaicinsu kan yadda ake takura ma musulmi wajen gina masallatai da suke gudanar da ayyukan ibadarsu.

Matasan sun daga hotunan masallatai na kasashen duniya daban-daban, inda musulmi suke gudanar da salla a cikin sahu.

652336



captcha