Bangaren kasa da kasa; Ministan harkokin wajen kasar Jamus ya bayyana kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki a matsayin wani mataki na tozarta 'yan adamtaka, tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa koyarwa irin ta addinin kiristanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar kasar hadaddiyar daular larabawa ta khalij an bayyana cewa, Ministan harkokin wajen kasar Jamus ya bayyana kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki a matsayin wani mataki na tozarta 'yan adamtaka, tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa koyarwa irin ta addinin kiristanci baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Jamus din ya ce kur'ani littafi ne mai tsarki da musulmi suke girmamawa, a matsayinsa na kirisa ta yaya zai amince a wulakanta littafin da shi ya ke girmamawa, a kn haka ba zai ji dadi a wulakanta littafin da wasu suke girmamawa ba.
652560