Bangaren kasa da kasa; Wakilan malaman addini mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait ya bayyana kiran da wani kiista ya yi a Amurka zuwa ga kone kur'ani da cewa, wani makirci ne yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar giso na jaridar kasar Kuwait ta Al-qabs an bayyana cewa, wakilan malaman addini mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait sayyid Muhammad Bahir ya bayyana kiran da wani kirista ya yi a Amurka zuwa ga kone kur'ani da cewa, wani makirci ne yahudawan sahyuniya da 'yan korensu a cikin kasashen yammacin turai.
Malamin ya kara da cewa yin kira zuwa ga kone kur'ani ba furuci ne da zai fito daga bakin mabiyin addinin kirist day a san addininsa ba, a kan haka masu yin wannan kira ba mabiya addinin kirista ba ne, ma'aikatan yahuwadan sahyuniyawa ne da suka lullube kansu da rigar addinin kirista.
652791