IQNA

Musulmin Jamus Na Allawadai Da Girmama Mai Tozarta Musulunci

12:15 - September 14, 2010
Lambar Labari: 1993532
Bangaren kasa da kasa; Kungiyoyin musulmi da dama a kasar Jamus sun yi Allawadai da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na girmama mutumin da ya yi zanen batunci ga addinin Musulunci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yeniasa an bayyana cewa, kungiyoyin musulmi da dama a kasar Jamus sun yi Allawadai da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na girmama mutumin da ya yi zanen batunci ga addinin Musulunci da kuma mabiyansa.

Kungiyoyin sun bayyana takaicin nasu ne a cikin wani bayani da suka fitar, da ke cewa suna yin Allawadai da girmama mutumin da ya yi zanen batunci ga manzon Allah (SAW) da waziriyar kasar Jamus Angela Mikel ta yi.

Bayanin nasu ya kara da cewa daukar irin wadannan matakai na tabbatar da cewa gwamnatin jamus tana goyon bayan cin zarafin addinin Musulunci da wasu makiyansa ke yi.

653386

captcha