IQNA

Matsayin Kungiyoyin Da Ba Na Gwmnati Ba Kan Karfafa Tattaunawar Addinai

17:04 - September 15, 2010
Lambar Labari: 1994894
Bangaren kasa da kasa; Kungiyoyi masu zaman kansu da ba na gwamnati ba za su iya taka gagarumar rawa kan karfafa tattaunawa tsakanin addinai da al'adu a kasashen duniya daban-daban.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na kungiyar habbaka harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO an habarta cewa, kungiyoyi masu zaman kansu da ba na gwamnati ba za su iya taka gagarumar rawa kan karfafa tattaunawa tsakanin addinai da al'adu a kasashen duniya daban-daban na duniya.

Kungiyar ta ISESCO ce ta tabbatar da hakan acikin bayanin bayan taron da ta gudanar kan bgatun tattaunawa tsakanin addinai na duniya, wanda aka fara tun shekarun da suka gabata, da nufin karfafa dangantaka da fahimtar juna tsakanin musulmi.

Tattaunawa tsakanin addinai na da matukar muhimmanci tsakanin al'ummomi mabiya addinai, da hakan kan ba su damar samun fahimtar juna.

654286


captcha