Bangaren kasa da kasa; Kone kur'ani mai tsarki makircin yahudawan sahyuniya ne da nufin haifar da rikici tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya, inda suka yi amfani da wani fetsararen mutum mai kiran kansa malamin addinin kirista a jahar Florida.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na han ko an bayyana cewa, masana daga kasashen musulmi da dama suna ganin cewa, kone kur'ani mai tsarki makircin yahudawan sahyuniya ne da nufin haifar da rikici tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya, inda suka yi amfani da wani fetsararen mutum mai kiran kansa malamin addinin kirista a jahar Florida a kasar Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa musulmi da ma wasu daga cikin kiristoci da suke adawa da wannan mataki na nuna kiyayya ga musulmi a cikin kasashen yammacin turai musamman a Amurka, suna ganin cewa yahudawan sahyuniya na son yin hakan ne domin samun damar mayar da musulmi saniyar ware a duniya.
654690